Trump yace Merkel mace ce mai karimci
March 17, 2017Shugaban Amirka Donald Trump a ganawarsa ta farko da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ziyarar da ta kai kasar yace yana goyon bayan kungiyar kawancen tsaro ta NATO amma kuma wajibi ne mambobin kasashe su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na biyan nasu kason kudin wajen tafiyar da kungiyar.
Trump ya kuma baiyana cewa yana fatan wanzuwar dangantaka ta adalci musamman ta fuskar manufofin cinikayya tsakanin Amirka da Jamus tare da jaddada goyon bayansa ga manyan hukumomin duniya wadanda ga alama sun hada da kungiyar tarayyar Turai da kuma kungiyar ciniki ta duniya WTO.
Ya yi watsi da zargin cewa yana neman ware kansa daga hadakar al'amuran kasashen duniya.
A nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce tana fatan ganin cigaban kyakkyawar dangantaka tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Amirka.