1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa kan jingine shirin nukiliyar Koriya ta Arewa

Ramatu Garba Baba
February 6, 2019

Shugaban Trump ya tsayar da ranakun da za su gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un, don tsara hanyar da za a bi a kokarin ganin bayan shirin makaman nukiliya da ya haifar da tsamin dangantaka a tsakaninsu.

Singapur USA-Nordkorea Gipfel Trump Pompeo
Hoto: picture-alliance/Zuma/Ministry of Communications

Shugaba Trump ne ya sanar da ranakun 27 zuwa 28 na wannan watan, inda ya ce za a yi zaman ne a kasar Vietnam, don ci gaba da tattaunawa kan samar da maslaha a yunkurin ganin Koriya ta Arewan ta amince ta kuma jingine shirin nukiliyarta.

Shugaba Kim Jong Un, a can baya,  ya yi alkwarin jingine shirin a yayin ganawarsu ta farko a kasar Singapore, amma kawo yanzu bai bayar da takaimaimen lokacin yin hakan ba ko wasu bayanai kan shirinsa na lalata makaman da aka ayyana a matsayin masu hadari ga duniya baki dayanta.