1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump zai gana da Putin a Amurka

August 9, 2025

Shugabannin kasashen biyu za su gana ne a ranar 15 ga watan Agusta a birnin Alaska na Amurka kan yakin Ukraine.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a birinin Alaska na Amurka a ranar 15 ga watan Agusta
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a birinin Alaska na Amurka a ranar 15 ga watan Agusta.Hoto: Sergey Guneev/SNA/IMAGO

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a birinin Alaska na Amurka a ranar 15 ga watan Agusta.

Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa ganawarsa da Putin gagaruma ce kuma za ta gudana ne a ranar Juma'a mai zuwa a Alaska.

Kasashen duniya na shirin samar da kudaden sake gina Ukraine

Babu wani cikakken karin bayani kan ganawar a sanarwar ta Trump, amma dai ana ganin batun tsagaita wuta a yakin Rasha da Ukraine ne zai kasance maudu'i.

Tun da farko a ranar Alhamis, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tabbatar da shirin ganawa da Trump kan yaƙin Ukraine, inda ya ce ya na ganin Hadaddiyar Daular Larabawa ce za ta kasance mai masaukin manyan bakin biyu.

An shafe sama da shekara uku ana gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine kuma Trump ya sha nanata burinsa na kawo ƙarshen yakin cikin gaggawa.

Manzon Amurka ya isa Moscow kan sulhunta yakin Rasha da Ukraine

A martaninsa, shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine ya fada cewa Ukraine ba za ta yi wa kundin tsarin mulkinta karan tsaye ba a kan batutuwan yankuna. Zelenskiy ya ce Ukraine ba za ta amince ta sallama yankunanta ga 'yan mamaya ba.

Shugaban na Ukraine ya fadi haka ne a matsayin martani ga sanarwar Shugaban Amurka Donald Trump ta ganawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin.

 Zelenskiy ya ce Ukraine tana shirye don samun mafita da za ta kawo zaman lafiya amma ba sallama yankunanta ba. Ya kara da cewa duk wata mafita da za a cimma ba tare da Kyiv ba, to mafita ce da ta saba wa zaman lafiya.