Trump zai gana da Xi Jinping kan kasuwanci
October 29, 2025
Shugaban Amurka Donald Trump ya sauka a kasar Koriya ta Kudu a wani bangare na karshe na ziyarar da yake yi a nahiyar Asiya, inda ya bayyana kwarin guiwar cimma yarjejeniyar kasuwanci da Shugaban China Xi Jinping, bayan ganawar da ya yi da Shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae Myung.
Trump ya bar birnin Tokyo zuwa Koriya ta Kudu sa'o'i kadan bayan da Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami da zai iya sarrafa makamashin nukiliya. Shugaban na Amurka yana shirin yin jawabi a taron kolin manyan jami'an gwamnati tare da ganawa da Lee a yankin Gyeongju.
Ofishin shugaban kasar Koriya ta Kudu ya ce zai yi maraba da Trump da kambin zinare mai kwafi tare da ba shi lambar yabo ta "Grand Order of Mugunghwa", kayan ado mafi girma a kasar.
Trump ya ce bayyana fatan ganin tattaunawarsa da Xi Jinping za ta yi armashi, wanda hakan zai kawo karshen yakin cacar baka na kasuwanci da bangarorin biyu ke yi da juna, tun bayan dawowarsa wa'adin mulki karo na biyu.