1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na matukar asara a harkar man fetir

August 28, 2024

A wani abun da ke zaman barazana ga burin miliyoyin al'ummar Tarayyar Najeriya na cin moriyar albarkatun man fetur, kasar ta hau ta kan gaba cikin tsadar hakar danyen mai a duniya baki daya.

Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

A tsawon watanni shidan da suka gabata kadai dai, Najeriyar ta kashe miliyoyin dalar Amurka wajen hakar man fetur din. Adadi mafi yawa a ko'ina a duniya, kuma kaso kusan 60 cikin 100 na dalar Amurka miliyan dubu 19 na kudin shigar kasar daga hajar danyen man a watanni shidan. A yayin da kasar take biyan dala 48 wajen hakar kowace ganga, mafi yawan kasashen da ke takama da hajar man kudin hako danyen man bai wuci dala 20 ba. Kasar Saudiyya ga misali, na kashe tsakanin dala biyu zuwa biyar wajen hakar kowace ganga yayin da kasar Angola ke kashe dala 20. Iran da Iraki ma dai, na kashe tsakanin dala 10-20 ne a kan kowace ganga. Dakta Garba Malumfashi dai na zaman tsohon jami'i a kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur a duniya, kuma ya ce yanayin da kasar take hakar man fetur na zaman mafi wuya a duniya baki daya.

Ko ya Najeriya za ta fita daga kangin tsadar hakar man fetur?Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

Da kyar da gumin goshi ne dai, tsohuwar gwamnatin Umaru Musa Yar'Adua ta kai ga kwantar da zuciyar mai tsumma cikin masana'antar da ta kalli tayar da kayar bayan matasan yankin Niger delta a lokaci mai nisa. To sai dai kuma ko bayan yanayi maras kyau cin-hanci a fadar Injiniya Mohammed Lawal da ke zaman tsohon dan kwamitin zartaswa na kamfanin NNPC, na zaman na kan gaba cikin tsadar da ke da tasiri ga rayuwa da makoma cikin kasar. Bakar hajar dai, na kan gaba a dogaron 'yan mulkin Najeriyar cikin harkokin yau da na gobe. Sai dai kuma an share shekaru cikin fatan man na iya kai kasar zuwa ga gacci, kafin sannu a hankali ta sake tunani da kila karkata zuwa iskar gas. Dakta Isa Abdullahi na zaman kwararre ga tattalin arzikin kasar, kuma ya ce da kamar wuya a cimma bukata ba tare da kai wa ya zuwa nazari mai zurfi a cikin masana'antar ba. Duk da cewar dai Najeriyar na da izinin hakar abun da ya kai kusan ganga miliyan daya da dubu 800 kullum, ya zuwa yanzun kasar na iya hakar abun da bai wuci ganga miliyan daya da dubu 300 ba kacal.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani