1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiTurai

Tsadar kaya a kasashe masu amfani da Euro

Abdullahi Tanko Bala
November 29, 2024

Farashin kayayyaki ya tashi a kasashen Turai masu amfani da kudin Euro

Takardun kudin Euro
Takardun kudin EuroHoto: picture-alliance/ZB

Tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki a kasashe 20 na kungiyar tarayyar Turai masu amfani da kudin bai daya na euro ya tashi da kimanin kashi 2.3% bayan da ya sauka zuwa 1.7% a watan Satumba. Sai dai kuma hakan ba zai sauya matsayin babban bankin tarayyar Turai na rage kudin ruwa ba.

Tashin farashin da aka samu shekara bayan shekara ya karu a watan Nuwamba da kashi 2.3% a bisa alkaluman da hukumar kiddidiga ta tarayyar Turai ta fitar.

Alkaluman sun nuna karin kashi 2% a watan Oktoba wanda ya dara abin da babban bankin tarayyar Turan ya fi fatan gani.

Sai dai kuma babu alamar  babban bankin tarayyar Turan zai dakatar da matakinsa kan ragin kudin ruwa, yayin da ya mayar da hankali wajen shawo kan tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin tarayyar Turan ke yi.