Farashin abinci kalubalen masu Azumi
May 3, 2019Talakawa dai a Najeriya duk lokacin Azumi kan dandana kudarsu gun 'yan kasuwa ta hanyar tsauwala wa kayayyaki kudi. Lokacin Azumi wani lokaci ne da bukatuwa ke kara yawa amma ba kasafai hanyoyin samu ke karuwa ba ga magidanta. Shinkafa na daya daga cikin abun da al'umma suka dogara da ita a matsayin abinci a Najeriya, to ko me ke sa hauhawar farashinta lokacin Azumi? Alhaji Musa Kalla mai Shinkafa Katsina shi ne uban kungiyar masu sayar da shinkafa a jihar ta Katsina:
"Sha'anin shinkafa gaskiya karatowar Azumi ta kara kudi kuma babu abun da ya kara mata kudi sai su masu kawowa daga can Nijar sun ce gwamnati suke biya haraji."
Baya ga shinkafa, dankalin Turawa da kwai da doya na daga cikin abubuwan da masu Azumi ke ta'ammali duk lokacin suma ba a bar su a baya ba wajen hauhawar farashin acewar Abdussalam Laima wani me sana'arsu.
To ko yaya talakawa ke ji da irin wannan tsadar kayayyaki lokaci Azumi? "Sunana Ibrahim Bala kamar dankali ma ni na hakura da shi ya fita raina kwata-kwata, saboda ina tunanin zan sai buhun shinkafa kwaya daya rak ance mun har an kara Naira 1200 duka kwana uku, abun ya munanamin zuciya har ma ni yanzu ban saya ba saboda jin takaici, dankali da ake sayar da shi 300 zuwa 400 wai yanzu har an wayi gari wai ya koma 750."
Gwamnati Najeriya dai na kokarin ganin ta dakile shigowa da shinkafar waje da nufin bunkasa noman ta gida, sai dai har yanzu akwai jan aiki domin yanzu haka sama da kashi tamanin cikin dari na shinkafar da ake siyarwa a jihar Katsina ta waje ce.