1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaKamaru

Kamaru: Tsadar nama saboda yajin aikin mahauta

Zakari Sadou LMJ
May 14, 2026

Yajin aikin da kungiyar mahauta ta kasar Kamaru ta shiga, ya fara jefa dubban 'yan kasa cikin damuwa musamman a manyan biranen Douala da Yaounde.

Kamaru | Yajin Aiki | Mahauta | Tsada | Nama | Shanu
Yajin aiki a Kamaru, ya haifar da tsadar nama musamman na shanuHoto: WDR

A kasuwar Sandaga shagunan nama na rufe, yayin da wasu kadan da suka bude ke sayar da kilo daya a farashin CFA 6,000. Pharel Aboubakar mahauci a kasuwar Sandaga da ke Douala ya shaidawa DW cewa: A baya da CFA 300,000 zuwa 350,000 mahauci zai iya samun dabbar yanka ya sayar da kilo 2,500 mai kashi, mara kashi kuma 3,5000 wanda hakan zai iya kara masa jari da zai ciyar da iyalansa. Amma cikin 'yan kwanakinan sai ka fitar da CFA 500,000 ya samu dabbar da zai iya samun kilo 140 zuwa 150, shanu masu daraja bujumai kuma 800,000 zuwa miliyan guda.

Karanci da tsadar nama a Kamaru, saboda yajin aikin mahautaHoto: Dragoslav Dedovic/DW

Wannan al'amari ya jefa magidanta cikin mummunan hali, sakamakon karancin nama a kasuwanni duk da cewa samun nama cikin abinci ya dogara ne da karfin aljihunka ko da kuwa a farashinsa na baya ya zama sai mai hali ne zai iya ci. A cewar mahautan, tsadar shanu ta samo asali ne daga karancin shigo da dabbobi daga Chadi da Nijeriya da kuma karin kudin sufuri da haraji a kan hanyoyi. Idan ba a samu mafita ba kafin karshen yajin aikin, ana fargabar mahauta za su tsawaita shi. Wannan lamari, ka iya kara dagula halin da kasuwar shanu da raguna ke ciki.

 

Gyarawa da wallafaawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani