1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsadar rayuwa a arewacin Najeriya

June 4, 2024

Al'ummar Arewacin Nigeria na cewa basu taba ganin tsadar kayan abinci kamar wannan lokacin ba abun da yasa da dama ke kwana da yunwa

Matsalolin tsaro da tsadar rayuwa a Najeriya
Matsalolin tsaro da tsadar rayuwa a NajeriyaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Al'ummar dai na cewa hanyoyin kashe kudade sun karu amma hanyoyin samunsu basu karu ba saboda kullum farashin kaya hauhawar yake a Najeriya, farashin yau daban na gobe daban.

Mata a nasu bangaren sun ce saboda halin da aka shiga na tsadar rayuwa dole suka rika taimakekeniya da mazaje amma duk da haka abun yaci tura.

A cewar masana harkokin tsaro irin su shehu Ladan, mahukunta Nigeria sai sun yi taka tsan-tsana matukar suna so su shawo kan matsalar tsaro da kasar ke fuskanta