Yarjejeniyar dakatar da yaki a Yemen
August 3, 2022Talla
Shekaru takwas ana aka yi ana yin yaki tsakanin dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan kawancen soji karkashin jagorancin Saudiyya da kuma 'yan tawayen Houthi dake samun goyon bayan Iran. Majalisar Dinkin Duniya, ta ce yakin da ake yi a kasar ta Yemen ya yi sanadin mutuwar dubban darurruwan mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu, inda kashi biyu bisa uku na al'ummar kasar ke bukatar agajin jin kai.