1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Tsagaita wuta a Lebanon na tangal-tangal

April 24, 2026

Yarjejeniyar tsagaiata wuta da Trump ya tsawaita a Lebanon na fuskantarr cikas, yayin da ake kila-wa-kala kan sake komawa kan taburin tattaunawa tsakanin Amurka da Iran.

Libanon Beirut 2026 | Zerstörung nach israelischem Luftangriff
Hoto: AFP

Yarjejeniyar tsagaiata wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita da makwanni biyu a Lebanon na fuskantarr cikas, inda kungiyar Hezbollah mai alaka da Iran ta sake zargin Isra'ila da sabawa ka'ida tare kuma da jaddada cewa tana da hakkin mayar da murtani. 

Sojojin Isra'ila sun ba da umarnin gaggawa a Juma'ar nan ga mazauna wani kuye a kudancin Lebanon da su fice daga gidajensu, a wani abu da ke zama karo na farko tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar.

Hakazalika ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta sanar da mutuwar mutane biyu a ranar yau, sakamakon wani hari da ta ce Isra'ila ta kai a kudancin kasar sa'o'i kadan bayan sanarwar Trump ta tsawaita yarjejeniyar.

A daidai wannan lokaci kungiyar Hezbollah ta bukaci gwamnatin Lebanon da ta janye daga duk wata tattaunawa kai tsaye da Isra'ila, tana mai gargadin cewa duk wata ganawa da bangarorin biyu za su yi ba za ta tsinana komai game da muradun al'ummar kasar ba.

A wani labarin kuma rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisa Dinkin Duniya da ke Lebanon ta sanar da mutuwar wani jami'inta dan asalin kasar Indonesia, sakamakon raunika da ya samu a kudancin kasar a karshen watan Maris.

Duk da halin da ake ciki, Trump ya ce yana da kwarin gwiwar za a yi ganawa a tsakanin firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu da  shugaban kasar Lebanon Joseph Aoun a makwanni masu zuwa, abin da zai kasasnce mai cike da tarihi ga kasashen biyu da ke yaki tun a 1948.