1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLibiya

Tsagaita wuta a Libiya

Usman Shehu Usman
August 16, 2023

An samar da tsagaita wuta a rikicin da ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya wa gwamnatin Libiya inda sabon rikicin ya hallaka mutane sama mkimanin 55

Libyen | Unruhen in Tripolis
Hoto: Yousef Murad/AP/picture alliance

An samar da tsagaita wuta a rikicin da ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya wa gwamnatin Libiya. Rikicin wanda shi ne mafi muni a bana, ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 55 yayin mutane kimanin 150 suka jikkata. Tun shekaran jiya ne dai fada ta barke ne tsakanin masu dauke da makaman na Libiya, bayan rashin jituwa da aka samu. Shugaban gwamnati a daya daga cikin gwamnatocin Libiya, Abdelhamid Dbeibah wanda MMD ke dauka a matsayin halartacce shugaban gwamnati, shi ne ya shiga tsakani aka samu sasanta rikicin. Kasar Libiya da tashin hankali ya mamaye, ta dan samu lafawar tashin hankali a baya-bayannan, amma kuma wannan rikicin ya nuna yadda har yanzu Tripoli na cikin wani gautsi da ko wane lokaci al'amura na iya rikidewa.