1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta a rikicin Ukraine

September 8, 2014

A na ci gaba da zama karkashin shirin tsagaita wuta a Ukraine, sai dai akwai fargabar da aka samu bayan wata musayar wuta da aka ji.

Hoto: Reuters/G.Garanich

A daren Litinin din nan dai dakarun gwamnati sun ce an ta harba musu bama-bamai, ko da ya ke kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa shaidun gani da ido sun ce duka bangarorin biyu da ke gaba da junan na mutunta yarjejeniyar. Hakananma kamfanin dillancin labaran kasar ta Ukraine Interfex ya bada rahoton cewa a ranar Litinin dinnan an sako dakarun sojan Ukraine 15 da ke hannun ‘yan aware. Sako dakarun dai na daya daga cikin tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaita wutar, kamar yadda jagoran na ‘yan awaren Alexander Sachartschenko ke cewa wannan shine daya daga cikin abinda suka tsara tun da fari karkashin yarjejeniyar.

"Da farko za mu fara mika sojojin yaki ga bangaren gwamnati ba tare da wani sharadi ba, muna fatan ita ma gwamnatin za ta sako mana firsinoninmu ba tare da bata lokaci ba, kuma muna dakon a sako mana tamkar adadin da mu ka mika.

Shugaban 'yan Awaren gabashin Ukraine Alexander SachartschenkoHoto: picture-alliance/dpa/M.Voskresenskiy

Yadda wasu ke kallon yarjejeniyar

Musayar wadannan dakaru daga kowane bangare na zaman wata alama da ke nuna yiwuwar kawo karshen tashin hankalin da ke kara lakume rayuka da asarar dukiya a tsakanin bangarorin biyu, sai dai wasu mazauna wannan yanki wandada kuma ke sharhi a kan wannan rikici na Ukraine cewa suke ai wannan tsagaita wuta babu inda za ta je.

"Wace tsagaita wuta? Wannan ai wasan kwaikwayone. Ina da tabbaci zan fada maka cewa a matsayina na masaniya kan kimiyar siyasa wannan yaki zai dauki tsawon shekaru biyar zuwa 10".

"Ina goyon bayan Novorossiya, wannan shine ra'ayina babu ruwana da mai suke tunani akai, babu wata tsagaita wuta nan gaba, saboda sun kashe mana 'yan uwan mu da dama"

Kakabawa Rasha sabon takunkumi

Ita kuwa Rasha wacce ake wa kallon kanwa uwar gami a wannan rikici na Ukraine wanda ya sanya Amirka da kawayenta na kasashen nahiyar Turai kakaba mata takunkumai, a ta bakin Firaminista Dmitry Medvedev yayin tattaunawar da aka yi da shi cewa ya yi cikin matakan da Rasha ke dauka na maida martini, za ta hana safarar jiragen sama na kasashe a sararin samaniyarta, a cewar sa sabon takunkumi da kasashen yamma suka kakaba mata aLitinin din nan babu abinda zai mata sai bata wata dama ta kara nazarin wasu hanyoyi da za ta bi wajen kara bunkasa kamar kasar China da a baya aka sanya mata takunkumai.

Firaministan Rasha Dmitry MedvedevHoto: Reuters

Yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a yammacin ranar Juma'ar makon jiya dai ta shiga cikin halin rashin tabbas a karshen mako biyo bayan musayar wuta a tsakanin bangarorin biyu da aka samu musamman lokacin da aka rika jin barin wuta a Mariupol birnin da ke kusa da gabar teku, sannan wani fadan ya faro a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Donetsk.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita:Lateefa Mustapha Ja'afar/PAW