1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta a rikicin Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 18, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin da ke yakar juna a Yemen da su tsagaita wuta, wanda tuni suka amince da tsagaita wutar ta tsahon sa'o'i 72.

YEMEN-CONFLICT-SANAA-STRIKES
Tsagaita wuta a rikicin YemenHoto: AFP/Getty Images

Tsagaita wutar dai za ta fara aiki a daren wannan Talatar 18 ga watan Oktoban da muke ciki. Tuni ma dai jakadan musamman Majalisar ta Dinkin Duniya a Yemen din Ismail Ould Sheikh Ahmed ya tabbatar da batun tsagaita wutar, wanda ya ce ana iya sake tsawaita shi. Rahotanni sun nunar da cewa sama da fararen hula 4000 ne kawo yanzu suka rasa rayukansu, tun bayan da Saudiya ta fara jagorantar rundunarta ta taron dangi wajen yin ruwan bama-bamai da makamai masu linzami a kasar cikin watan Maris na shekarar da ta gabata ta 2015, a abin da ta kira yunkurin kare shugaban kasar Abdrabbuh Mansour Hadi daga yunkurin kifar da gwamnatinsa da 'yan tawayen Houthi ke yi.