Tsagaita wuta a Sudan ta Kudu
May 5, 2014Rahotanni daga birnin Addis Ababa na kasar Habasha sun ce, gwamnatin Sudan ta kudu da 'yan tawayen kasar, sun samu nasarar rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita wuta, ta tsawon wata guda daga yau Litinin. Domin baiwa fararen hullar da ke cikin tsaka mai wuya a kasar, damar samun maslaha tare kuma da baiwa kungiyoyin agaji damar shiga da kayayyakin abinci, ga 'yan gudun hijirar da yawan su a halin yanzu ya kai fiye da miliyan guda.
Wannan yarjejeniyar ta biyo bayan ziyarar da Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya kai a kasar ta Sudan ta Kudu, kasar da kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suka ce ta na fuskantar hatsarin yunwa.
A yau ma dai John Kerry ya kara jaddada matakin Amirka na daukan tsauraren matakai kan shugaban 'yan tawayen kasar Riek Machar. Muddin dai ya ki lamunta da bada hadin kai wajan samun zaman lafiya. Inda a yau ma aka gwabza fada a yankin Bentiu babban birnin yankin da ke da arzikin man fetur na wannan kasa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Usman Shehu Usman