Tsagaita wuta a yakin kasar Siriya
February 7, 2014Yarjejeniyar za ta taimakawa fararen hular ficewa da suka hadar da mata da kanan yara da wadanda suka samu raunuka da kuma tsofaffi daga garin na Homs. Da yake tabbatar da cimma wannan yarjejeniya, kakakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq yace.....
"Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin bada agaji sun samar da abinci da magunguna da kuma saurna ababen bukata a wajen garin na Homs domin taimakawa wadanda suke cikin bukatar agaji. Da zarar mun samu amincewar bangarorin biyu cewa a kwai damar shiga domin bada kayan agajin zamu shiga aiki gadan-gadan. Mun kuma tanadi ma'aikatan agaji".
A nata banagaren shugabar hukumar bada agajin gaggawa Valerie Amos, ta yi maraba da wannan ci-gaban da aka samu wanda tace zai taimakawa fararen hular da yaki ya rutsa da su su fice domin tsira da rayukansu, yayin da a hannu guda kuma zai bada damar shigar da kayan agaji ga kimanin mutane 2,500 da yakin ya rutsa da su a wasu yankunan garin na Homs tun a tsakiyar shekarar 2012.
Kawo yanzu dai rahotanni sun tabbatar da cewa an samu tsagaita wuta a garin na Homs kamar yaddad yarjejeniyar ta tanada domin fararen hular su samu su fice daga garin.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu