Tsagaita wuta ya fara aiki Sudan
April 25, 2023Talla
Wanna ya samu ne biyo tsagaita wutan kwanaki uku da aka samu, inda dubban mutane suka fada tsakiyan yaki. An dai fara aiki da yarjejeniyar tsaigata wuta ta kwanki uku, wace kasashen Amirka da Saudiya suka jagoranci cimmawa. Kungiyoyin bada agaji sun sanar da cewa yanayin jinkai a kasar Sudan ya yi matukar muni fiye da yadda ake zato. Sama da kwanaki goma ana luguden wuta a biranen kasar ba kakkautawa, abin da ya jawo yakin ya shafi al’umma da yawa. Fadan dai ya fi muni ne a Khartoum babban birnin kasar da kuma Omdurman. Yanzu haka dai kasashen duniya na kai kawo don kwashe jama’arsu daga Sudan.