SiyasaYuganda
Yuganda: Tsaiko yayin gudanar da zabe
January 15, 2026
Talla
Wasu rumfunan zaben na Yuganda sun ma kasance ne a rufe tsawon sa'o'i, yayin zaben da aka shirya fara shi da karfe bakwai na safiya, abinda Hukumar Zabe ta Kasa ta bayyana da tangardar na'urori da ta samu. An dai gudanar da zaben cikin fargaba da kuma katsewar sadarawa ta Internet tsawon kwanaki, abin da ya saba da tsarin dimukuradiyya. Shugaba Yoweri Museveni da ke da shekaru 81 a duniya da ke mulkar kasar tun daga shekara ta 1986 na neman tazarce, a zaben da babban abokin hamayyarsa ya kasance mawaki Bobi Wine da ke da shekaru 43 a duniya, wanda kuma ke neman sauyi a siyasar kasar.