Sabuwar dokar Vladimir Putin na cinikin gas
April 1, 2022Dokar cinikayyar da Putin ya sanya wa hannu a ranar Alhamis da ta gabata, ta tanadi cewar kasashen da ba su dasawa da Rasha da ke sayen makamashin iskar gas daga Rashan, za su bude asusu a cikin bankunan Rasha don biyan kudin makamanshin da kasar ke sayar musu da kudin ruble daga wannan asusun.
Shugaban yayi gargadin cewa, kin mutunta dokar na nufin kwangilar da ake yi a tsakaninsu a halin yanzu za ta kasance an dakatar da ita.
A daya bangaren kuwa, a wannan Juma'ar Tarayyar Turai ke taron koli inda batun yakin da ake zai mamaye taron, kungiyar za ta nemi hadin kan Chaina don kada ta taimaka wa Rasha a mamayar Ukraine saboda takunkuman da EU ta sanya wa Rashan yayi tasiri.
Akwai kuma batun neman Chainan ta shawo kan Shugaba Putin don kada yayi amfani da makami mai guba a yakin kamar yadda yayi barazanar yi.