1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka a tsakanin Amirka da Rasha

August 8, 2013

Fadar gwamnatin Rasha ta yi Allah wadai da soke ganawar Obama da Putin.

U.S. President Barack Obama (L) meets with Russian President Vladimir Putin during the G8 Summit at Lough Erne in Enniskillen, Northern Ireland June 17, 2013. REUTERS/Kevin Lamarque (NORTHERN IRELAND - Tags: POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY)--eingestellt von haz
Hoto: Reuters

Fadar Kremlin ta shugaban kasar Rasha, ta bayyana takaicinta dangane da sanarwar da Amirka ta fitar, ta soke wata ganawar da shugabannin kasashen biyui suka shirya yi a watan Satumba, domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafesu, bisa abin da fadar gwamnatin Amirka ta White House ta ce, rashin samun ci gaba ne a kan batun Edward Snowden, tsohon jami'in hukumar leken asirin Amirka da gwamnatin Rasha ta baiwa mafakar siyasa. Mai baiwa shugaban Rasha shawara a kan hakokin da suka shafi kasashen ketare, ya ce wannan matakin, ya nuna cewar, Amirka ba ta kaunar yin mu'amala da Rasha a matsayin wadanda ke da matsayi iri guda. Sai dai a nashi bangare, shugaba Obama ya zargi fadar gwamnatin kasar ta Rasha da komawa ga zamanin yakin cacar-baka. Idan za ku iya tunawa dai, a makon jiya ne Rasha ta baiwa Snowden mafakar siyasa - ta wucin gadi, tare da yin watsi da bukatar Amirka ta neman a mikashi domin ya fuskanci shar'iar cin amanar kasa, bisa bayanan sirrin da ya kwarmata wa duniya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu