1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin Holland da Turkiya

Zainab Mohammed Abubakar
March 12, 2017

Daruruwan Turkawa ne suka gudanar da gangami a kofar karamin ofishin jakadancin Netherlands da ke birnin Istanbul da safiyar wannan Lahadi, a daidai lokacin da huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu ya dada tabarbarewa.

Niederländisches Konsulat in Istanbul
Hoto: picture alliance/abaca/A. Coskun

Mahukuntan Netherlands din dai sun hana ministan harkokin wajen Turkiyya sauka a birnin Rotterdam a jiya Asabar, a ci gaba da nuna adawa da yunkurin neman goyon bayan Turkawa da ke zaune a ketare, kan tsawaita wa'adin mulkin shugaban Tayyip Recep Erdogan. Murat Saglam na daya daga cikin Turkawa masu gangamin...

" Me zan iya cewa? Wannan abun kunya ne a bangaren Turai. Babban abun kunya. Wannan lokaci ne da aka yi wa demokradiyya karan tsaye. Bai dace a yi wa wani ministan Turkiyya ko kuma na wata kasa irin wannan cin fuska ba".

Ministar kula da iyali ta Turkiyya Fatma Betul Sayan Kaya da ta yi kokarin ganawa da masu gangamin goyon baya ga shugaba Erdogan a birnin Rotterdam a jiya da maraice,  ta tsinci kanta a kan iyakar Jamus.