Tsamin dangantaka tsakanin Jonathan da Obasanjo
December 23, 2013Ta dai fara daga karamin ƙani zuwa yayansa. Bayan dubun gaisuwa da fatan duk lafiya. Ka tilasta ni ka matsa min lamba, har ka kai ni ga gindin magarya ta tuƙewa kafun fara tunanin ya kamata in fara, har mutane su san nawa bangaren domin yanke wa kansu hukunci.
Babban yayana na yi tunanin babu bukatar maida martani ga jeri na wasikun ka. Da wasunsu ke kama da kokarin murde wuya, wasu ma sun jibanci barazana ga tsaron kasarmu ta Najeriya. Amma dai tun da ya kai tsami ta lalace a tsakanin mu, to ka sani kauda kai kawai na kai ga yi ga jeri na zarge-zargen da a ke yadawa a ƙasa.
Na dai sani akwai matsala ta tsaro da zaman lafiya, to amma ka sani na samu gagarumi na ci-gaba a kokari na kawo karshen ta. Boma-bomai sun kamfa haka tashe-tashen hankula sun yi kasa, amma dai kuma ka sani matsalar ta faro tun a zamanin da ka ke fada kowa ya yi zawo. Amma ka bari lamarin ya girma har ya wuce gona da iri.
Bani da niyyar murkushe al'umma irin wadda ka yi wa kauyukan mu na Odi a Bayelsa, haka kuma mun yi kokari na rarrashi da nufin jawo yan kungiya ta Boko Haram bisa ga teburi. Na ji ka yi batun cin-hanci, nan ma ka sani ba ni ne farau ba. Kuma ma ina kalubalantar ka da tabbatar da kawo shaidun da ka ke ikirari.
Ban kuma manta da kokari na ruda al'amura da zagon kasa ga jam'iyyar mu ta PDP, to ai kai ne a gaba, don kai ka kori kusan kowa. Kai ne ma ka ɗiga mata dambar rikicin da ke barazana gare ta a halin yanzu.
To sai dai kuma daga dukkan alamu shugaba Goodluck din da ya share shafuka yana kokarin maida martani ga tsohon mai gidan sa dai, na da sauran tafiya kafin ya iya burge masu adawar kasar da ke masa kallon magana ta ɗara aiki. Isyaku Ibrahim dai na zaman jigo a cikin jami'iyar APC, mutumin kuma da ke cewar fa karatun na Jonathan bai wuci surutun gindin mai shayi ba.
Fada tsakanin uban gida da yaron sa ko kuma kokari na kare kai a bisa jeri na kwararan zargi dai, sannu a hankali kasar ta Najeriya na fiskantar wani sabon salon siyasa, ta wankan datti a cikin talakawan kasar da aka dade ana yi wa suddabarun, sun kusan isa tudun muntsira.
Siyasar kuma da ke daɗa fiddowa a fili da irin dattin da barnar da shugabannin kasar suka dauki tsawon lokaci suna tafkawa.
Abun da kuma a cewar Bello Sabo Abdulkadir da ke zaman jigo a cikin jamiyyar PDP mai mulkin, ke zaman alamu na rushewar tsarin shugabancin kasar ta Najeriya, kuma ke bude ido ga ragowar al'ummarta.
Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba a cikin siyasar ga Tarrayar Najeriyar da sannu a hankali ke daɗa matsantar zabuka cikin rikici na masu siyasar tata da kuma rudanin rashin tsaron al'ummarta.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman