1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lebonon: Bukatar minista ya yi murabus

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 4, 2021

Firaministan Lebanon ya sake jaddada kiransa ga ministan yada labaran kasar ya yi murabus daga mukaminsa.

George Kordahi | libanesischer Informationsminister
Ministan yada labaran Lebanon George Kordahi Hoto: Bilal Hussein/AP Photo/picture alliance

Wannan dai na zuwa ne bayan wasu kalamansa kan rundunar taron dangin da saudiyya ke jagoranta a kasar Yemen, abin da ya jagoranci tarbarbarewar dangantakar Lebanon din da Saudiyyan. Rikicin dai na neman wargaza sabuwar gwamnatin ta Berut, tare da kara ta'azzara matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki a yanzu.

Firaminista Najib Mikati dai, ba shi da 'yancin korar ministan yada labaran ba tare da amincewar kaso biyu bisa uku na majalisar zartarwar kasar ba. A nasa bangaren minista n yada labaran George Kordahi ya ki neman afuwa balle ya yi murabus daga mukaminsa, wanda ke samun goyon bayan kungiyar Hezbollah da mukarrabanta na majalisar zartarwa.