1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantakar Saudiyya da Masar

Usman ShehuApril 29, 2012

Ƙasar Saudiyya ta janye jakadanta a Masar bayan dubban jama'a sun yi bore a gaban ofishin jakadancinta, wanda shine matakin farko tun hambare Mubarak

Saudi King Abdullah bin Abd al-Aziz, left, directs Egyptian President Hosni Mubarak, second right, Iraqi President Jalal Talabani, right, and Amr Moussa, Secretary General of the Arab League, second left, during a group picture of Arab leaders before their summit in Riyadh, Saudi Arabia, Wednesday, March 28, 2007 which is expected to focus on how to revive Middle East peace efforts. (AP Photo/Amr Nabil)
Sarki Abdullah na Saudiyya da tsohon shugaban kasar Masar Hosni MubarakHoto: AP

Ƙasar Saudiyya ta janye jakadanta, kana ta rufe ofishin jakadancin ta dake ƙasar Masar. Kamfanin dillalcin labaran Saudiyya ya ruwaito cewa an dau matakin ne don dalilan tsaro, inda masu bore suka kewaye ofishin jakadanci Saudiya a birnin Alƙahira, a martani bisa tsare wani Lawya ɗan ƙasar Masar wanda Saudiyya ta yi a lokacin da ya je yin Umrah. Wani kakakin gwamnatin Saudiyya yayi tir da masu boren, wadanda aƙalla suka kai dubu daya da suka yi dafifi a gaban ofishin jakadancin, kuma yace sun sun nufi kutsawa ciki.

Shugaban gwamnatin sojin Masar ya maida martani inda yace yana kan war-ware matsalar da taso. Saudiyya dai ta tsare Lawyan dan ƙasar Masar bayan da ya furta cewa yakamata a kafa mulkin demokraɗiyya, inda nemi yan Saudiyya suma sun yin boren ganin bayan mulkin kama karya tamkar na yan Masar, abinda gwamnati Saudiyya ta yi Allah wadai da shi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tanko Bala