1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantakar siyasa a Nijar

Abdoulaye Mamane AmadouJanuary 6, 2015

'Yan adawar Nijar din dai na zargin bangaren gwamnati da cin hanci da karbar rashawa tare da yunkurin wargaza jam'iyyun adawar kasar.

Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

A baya-bayan nan dai 'yan adawar kasar sun dauki matakan kauracewa duk wani goron gayyatar da bangaren masu mulki ya yi musu, saboda dalilai na siyasa.

To sai dai a nata bangare, jam'iyyar PNDS tarayya dake mulki na mai ganin rashin abun fadi ne kawai ke ga 'yan adawar. Wannan lamari na faruwa ne a yayin da ake shirin tunkarar zabubbuka a kasar a shekara ta 2016 mai gabatowa.

Tsamin dangantakar dai ya faro ne tun lokacin da masu adawa a Nijar din suka zargi bangaren mulkin da rashin iya jagoranci da cin hanci da rashawa da yin almundahana da dukiyar kasa har da kokarin wargaza jam'iyyun adawa a kasar da nufin ci gaba da kasancewa a kan mulki.

Abdoulaye Mamane Amadou