1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanyin hunturu a arewacin Najeriya

January 7, 2020

Jihar Sokoto daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsanancin sanyi lamarin da yasa al’umma kokawa.

Nigeria Sultanspalast in Sokoto
Hoto: DW/T. Mösch

Tsananin sanyin da ake fama dashi a jihar Sokoto kusan ya kai ga matakin takaita zirga-zirga da kuma hana walwalar al’umma abin da ya haifar da takaita ayyukan wasu sana’oin.

Daga cikin sana’oin da sanyin ya shafa har da sana’ar Kabu-kabu kamar yadda wani matashin dake sana’ar Kabu-kabun ya shaidawa DW

Tsananin sanyin da ake fama da shi ya tilasta wa masu gidajen wanka tanadar ruwan zafi don biyan bukatun kwastomominsu inji Umaru Usman wani mai gidan wanka a birnin Sokoto.

Masana lafiya sun tabbatar da cewa tsanantar sanyi kan haifar da cututtuka da dama da suka hada da fashewa ko kuma tsagewar kafa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani