Spaniya da Faransa na fama da wutar daji
July 17, 2022Talla
A Faransa sama da mutum dubu 14 ne gobarar dajin ta tilasta wa barin matsugunansu, tsananin zafin da ya haura maki 40 a ma'aunin Celciues a wasu kasashen, masana na cewar ya buso ne daga nahiyar Afirka.
Tun bayan da zafin ya tsananta a kasar Spaniya an sami mutuwar mutane 360 a tsukin kwanaki biyar.
Gobarar daji a wannan shekarar ta yi saurin zuwa, lamarin da ke kara nuna kamarin sauyin yanayi .