Ana yin zafi mai tsanani a Turai
June 25, 2019Talla
A Faransa inda a yau a wasu sasan kasar matsayin zafin ya kai maki 35 a ma'aunin Celicius, kwarraru sun ce zai haura da maki 41 a cikin makon. Masu yin hasashe a kan yanayi sun ce a tsakiyar wannan mako a Jamus za a yi tsananin zafin ranar da ba a taba yin irinsa ba a cikin shekaru 70. Yayin da a kasashen Beljiyam da Spain da Ostiriya can ma zafin ranar zai haura.