Ciyar da dalibai a makarantun Kano
February 17, 2016Wannan shiri na ciyarwa Kwamitin Kyautata da'a da aka fi sani da CRC na jihar Kanon ne ya rika aiwatar da shi a makarantun furamaren kuma ya taimaka wajen samun karin yaran da ake turawa makarantun.
Karamar Hukumar Gwale na daya daga cikin kananan hukumomin da suka fi amfana da shirin saboda yawan yaran da ke shiga makarantun Furamaren.Malam Abdullahi Zubair Abiya ne shugaban karamar hukumar da ya tabbatar da hakan.
"Kamar yadda ka gani muna magana da yaran nan suna murna an ce a ci gaba da ba su abinci kuma suna jin dadi.To wannan zai sa yaro ya zo makaranta ya tsaya ya ci abinci.Ko yaya dai yana samun canji na abincin. Idan a gida ya ci abinci kuma idan ya zo makaranta ya sami wani abinci ya ci zai fi jin dadinsa kuma zai taimaka masa wajen karatu."
To amma duk da tarin wannan fa'ida me ya jawo tsaikon shirin?A cewar Malam Sagir Gambo 'Yan Musa ba dakatar da shirin aka yi ba face yin gyaran da zai dace da tashin farashin kayan da ake samu.
"Mu a nan jihar a kan Naira goma sha hudu ake ciyar da yaran nan sannan kuma a kasuwa abubuwa duk inda ka je shinkafar da ake sayarwa Naira dubu bakwai yanzu ta kai wajen dubu tara ko goma ma. Irin waken da ake dan saya kwano Naira dari uku yanzu ya kai Naira dari biyar da wani abu. Abubuwa dole ka tsaya ka sake lissafi ka ga ya zaka yi ka kyautata abincin yara kowa ya ci ya koshi".
An zabi Makarantar Furamare ta Dandago mai tarihi don kaddamar da shirin na ajujuwan keso na renon kananan yaran, yayin da a ke sa ran nan gaba kadan ita ma gwamnatin tarayyar Najeriya za ta yi hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi wajen gudanar da wannan shiri na ciyarwa.