Tsaro a Banjul bayan yunkurin juyin mulki
December 30, 2014Sojojin kasar Gambiya sun katse zirga-zirga a kan babbar gadar da ta hade fadar shugaban kasa da tsakiyar babban birnin kasar wato Banjul, bayan da aka shafe daren jiya ana musayar wuta a kusa da fadar shugaban kasa. Wannan rikici dai ya barke ne a daidai lokacin da shugaba Yahya Jammeh yake ziyara a kasar Faransa.
Kafafen watsa labaran Gambiya sun danganta abin dake faruwa da yunkurin juyin mulki daga sojojin dake bore. Sai dai har yanzu hukumomi ba su ce uffan ba game da wannan batu. Mazauna birnin Banjul sun bayyana cewa bankuna da kuma ma'aikatan gwamnati sun kasance a rufe a wannan Talatar.
Shi dai shugaba Yahya Jammeh ya haye kan kujerar mulki ne tun shekaru 20 da suka gabata sakamakon wani juyin mulkin da ya aiwatar. Kasashen waje na zarginsa da take hakkin bil adama da gallazawa 'yan adawa da kuma 'yan jarida.