Tsaro ne kan gaba a ziyarar Trump a Gabas ta Tsakiya
May 19, 2017Wannan ziyara ta shugaban Amirka Donald Trump dai ita ce ta farko dai zai kai wata kasa tun bayan da ya dare kan gadon mulki kuma zai fara ne da Saudiyya kafin daga bisani ya isa Isra'ila. Ana dai kallon wannan ziyara a matsayin ta tarihi domin tun lokacin da tsohon Shugaba Jimmy Carter ya dauki madafun iko zuwa yanzu duk wani shugaban Amirka ya kan fara ziyara zuwa kasar Mexico ko Kanada ko kuma wata kasa a nahiyar Turai amma Shugaba Donald Trump ya zama na farko da ya saba wannan al'ada domin fara ziyara zuwa kasar Saudiyya sai dai ziyarar ta zo lokacin da Shugaba Trump ya ke fuskantar matsalolin siyasa a cikin gida.
Yayin wannan ziyara dai Shugaba Trump zai gana da Sarki Salman na Saudiyya da sauran manyan jami'ai na masarautar tare da ganawa da sauran shugabannin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya. Akwai magana game da dakile masu matsanancin ra'ayi da ake dangantawa da addinin Islama kuma a ganin Nile Gardiner da ke gidaudiyar Heritage ta masu ra'ayin mazan jiya abin tambaya shi ne inda manufofin gwamnatin Shugaban Donald Trump na Amirka suka karkata don a cewar Nile ''ana sake komawa dangantaka da aka saba tsakanin Amirka da yankin Gabas ta Tsakiya sabanin yadda lamarin ya ke a baya don tsohon shugban Amirka Barack Obama bai yi wani kazar-kazar ba kan dantankata da kasashen yankin."
Akwai masana da ke goyon bayan tsohon Shugaba Barack Obama na kasar ta Amirka wadanda suka soki wannan ziyara ta Trump kuma suke gani babu yadda za a kwatanta ziyarar da irin wadda tsohon Shugaba Obama ya kai zuwa birnin Alkahira na Masar a farkon hawansa mulki a shekara ta 2009 saboda yadda ya mayar da hankali lokacin jawabinsa kan hare hakkin dan Adam da mata cikin kasashen Larabawa da na Musulmai.