1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus za ta sake tsawaita bincike kan iyakokinta

Abdourahamane Hassane
August 7, 2025

Jamus za ta sake tsawaita bincike kan iyakokinta na wucin gadi, in ji ministan cikin gidan Alexander Dobrint.

Hoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

Ministan cikin gida na Jamus  Alexander Dobrint; ya ce yin hakan wani mataki na yaki da bakin haure, lamarin da ya haifar da cece-kuce tsakanin kasashen da ke makwabtaka da kasar.

Jamus ta sake kafa bincike na wucin gadi a dukkanin iyakokinta a ranar 16 ga watan Satumba, na shekara ta 2024, na tsawon watanni shida a zamanin mulkin Olaf Scholz, kafin sabon firaminista  Friedrich Merz  ya karfafa binciken kan iyakokin:

Bisa alkalumman da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamus ta fitar, an mayar da jimillar mutane sama da dubu tara a kan iyakokinta tsakanin takwas ga watan Mayu zuwa 31 ga watan Yuli na wannan shekara.