Najeriya za ta tsaurara dokokin fyade
June 11, 2020Kama daga jihar Kano da a wannan mako aka kama wani mutum guda daya da yi wa mata 40 fyade cikin gari daya ya zuwa Anambra inda aka samu kimanin iyaye 80 sun yi wa 'ya'yansu fyade a cikin kullen Covid-19.
Can a jihar Edo ma dai an kai ga halaka wata budurwa bayan yi mata fyade a harabar wata majami'a cikin jihar a makon da ya shude. Tuni aka samu ta'azzarar al'adar fyade a ko'ina cikin Najeriya ya zuwa yanzu.
To sai dai kuma gwamnatin kasar tace daga yanzu kuma duk wanda aka samu da laifin aikata fyade a cikin tarrayar najeriya to zai fuskanci tsanani na hukunci kama daga dauri na rai da rai ya zuwa hukunci na kisa kamar yadda dokar hana fyade ta kasar ta tabbatar.
Pauline Tallen ministar mata ta Najeriya ta ce yawan karuwa kan fyade a kasar ya nunka har gida uku sakamakon zaman gida na Covid-19. Kuma a fadar ministar matan lokacin jan shari'a ko kuma yanke hukuncin tara ya kare ga masu al'dar fyaden kama a bangare na gwamnatin tarayya ko kuma su kansu jihohi na kasar.
Abun jira a gani dai na zaman yadda matakan 'yan mulkin ka iya shawo kan annobar da ke neman komawa ruwan dare gama duniya a kasar bisa hujjojji iri-iri.