Corona ta yadu zuwa kasashe 195
March 24, 2020Talla
Wani sakamakon bincike da ya fito yau Talata na nuni da cewar, killace wadanda suka harbu, nisanta juna a wuraren aiki da inda jama'a ke haduwa da rufe makarantu, sun kasance matakai masu inganci wajen yaki da yaduwar cutar COVID-19, bisa la'akari da martanin kasar Singapore kan wannan cuta mai kisa.
Masu bincike daga jami'ar Singapore sun ga yadda nisanta juna tsakanin mutane uku a lokaci guda, ya yi tasiri wajen rage yaduwar Corona tsakanin al'ummar kasar.