1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta tsawaita takunkumi kan Rasha

Suleiman Babayo
December 16, 2016

Tarayyar Turai ta tsawaita takunkumi kan Rasha har zuwa tsakiyar shekara mai zuwa ta 2017, bisa rikicin gabashin kasar Ukraine.

Belgien | EU-Gipfel | Dalia Grybauskaite, Klaus Werner Lohannis, Paolo Gentiloni  und Nikos Anastasiadis
Hoto: picture-alliance/abaca/D. Aydemir

Kungiyar kasashen Tarayyar Turai EU ta amince da shirin tsawaita takunkunmin da suka kakaba wa Rasha saboda mamaye yankin Kirimiya da ke gabashin Ukraine, a yayin taron kungiyar da ya gudana a birnin Brussels na Belgium. Za a ci gaba da aiki da takunkumin kan bangorin tsaro da makamashi gami da tattalin arzikin kasar ta Rasha har zuwa watan Yulin shekara ta 2017.

Shugabannin sun dauki wannan matakin ne sakamakon abin da suka kira yadda kasar ta Rasha take jan kafa wajen aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da Tarayyar Turan kan shawo kan rikicin gabashin Ukraine din. Amma takunkumi bai kunshi matakin Rasha na goyon bayan gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad da kasashen Yammaci suke zargi da kama karya ba.