1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsayar da Shettima zai shafi hulda da Amurka?

Ubale Musa Lateefa Mustapha Jaafar
July 10, 2026

A wani abin da ke iya sauya da dama a cikin gidan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya amince da ci gaba da aiki tare da mataimakinsa Kashim Shettima a zabe na gaba.

Najeriya | Siyasa | Takara | Kashim Shettima | Zabe | 2027
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim ShettimaHoto: Ken Ishii/REUTERS

An dai dauki lokaci ana kai kawo a tsakanin sauke Kashim Shettima da maye gurbinsa da wani Kirista daga sashen arewacin Najeriyar, bayan matsin lambar Amurka ta kokarin kare Kiristocin kasar. Wani taron jam'iyyar APC a Abuja dai, ya tabbatar da ci gaban na Shettima a wata takardar da shugaban ya mikawa uwar jam'iyyar. Ganawar sirri tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakin nasa suka yi, ta kare da Shettiman fita cikin raha da annashuwa.

Matsin lamba daga ketare

An yi hasashen yiwuwar ci gaba da Shettiman da ya fuskanci tsawon lokaci cikin rashin tabbaci, sakamakon matsin lambar kasashen waje. Sai dai kuma a yayin da wasu ke tsallen murna a APC daga dukkan alamu zabin Tinubun na shirin zama koma-baya a tsakanin 'yan jam'iyyar da ke tunanin sirkawa da nufin biyan bukatar Amurka ta kare Kirista. An ambato sunan ministan tsaron kasar Janar Christpher Musa daga Arewa maso Yamma.

Yan Najeriya su tashi su karbi kasarsu - MC Tagwaye

04:33

This browser does not support the video element.

An kuma  kira sunan tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara daga Arewa maso Gabas, cikin wadanda ke iya maye gurbin na Shettima. Ko bayan matsin lambar Turawan dai, makusantan Tinubu sun dauki lokaci suna nazarin tasirin tikitin Musulmi guda biyu da ya dora shugaban bisa mulki daga farkon fari. Tinubu na kara bakin jini a sassan na Arewa biyu, bayan zargin karuwar talauci da ma ta'azzarar rashin tsaro a karkashin mulkin nasa.

Ya dangantaka da Amurka za ta kaya?

Ko  ya take shirin da ta kaya a tsakanin masu tunanin sauyin na  APC da kuma masu fadin a dora zuwa gaba, sake tsayar da Shettiman na kara fitowa da burin shugaban na samun nasara maimakon burge wasu sassa ciki da ma wajen kasar. In har shugaban ya fifita batun nasarar zabe dai, akwai alamun shakku kan makomar danganta da kasar Amurka. Magoya bayan Donald Trump sun dauki lokaci suna matsin lamba, kan sauya Shettiman da Kirista da nufin bayar da kariya ga miliyoyin Kiristocin kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani