Tseren dawakin Filingue da ke Jamhuriyar Nijar
February 17, 2026
Da kafrko dai al'umma ce ta gundumar Fillingue da ake kira yankin Kourfey da ke cikin jihar Tillabery ne, suka hadu suka kirkiro da wadannan wasanni da aka kira 'Dokin Iska Dan Filingue'.
Domin tunawa da tarihin dokin da kuma al'adun yankinbaki daya wanda a yanzu gwamnati musamman ma ofishin ministan al'adu da wasannin motsa jiki suka karbi wannan wasa a hannunsu a matsayin wasa na kasa ganin yadda ake kokarin farfado da al'adu na kowane yanki a kasar ta Nijar.
Tasirin gasar
Baya ma dai da sukuwa kaman yadda aka sani na dokin iska dan Filingue wanda a baya ya yi suna wajen sukuwa, akai kuma taruka na fadakarwa da sauran laccoci da ake yi, inda a wannan karo an yi zaman tattaunawa da fadakarwa kan zaman lafiya a daura da wasan na Dokin Iska dan Filingue. Salissou Saddi, shi ne magatakardan Majalisar matasa ta gundumar Filingue ya ce ya ji dadin ganin yadda matasa suka kasance sahun gaba a cikin wannan wasa na al'adun.
Bayan ma matasa suma dai mata ba a barsu a baya ba, wanda a cewar shugaban gamayyar kungiyoyin matan Kourfey Madame Zalia Samey, tunda yanzu aka ce za a karfafa al'adu na gargajiya ta hanyar wannan wasa na Dokin Iska Dan Filingue lalle an dauki hanyoyi na gyraran tarbi'a a nata gani.
Kudirin bikin gasar tseren dawakin
A ranar 11 ga watan Oktoba ne dai na 2025 aka dauki kudirin kafa bikin Dokin Iska Dan Hillingué, inda wannan karo na tara ya zamana na farko a kalkashin kulawar gwamnati.
Bikin dai ya kunshi jawabai da dama, musamman na Ministan Al'adu, Sidi Mohamed, da Gwamnan jihar Tillabéri, Kanar Maina Boukar, zuwa mai martaba Sarkin Kourfey Saley Boubacar Marafa, da sauran manya-manyan baki da aka gayyata kuma suka amsa domin daukaka wannan wasa na Al'adun Kurfey na Dokin Iska Dan Filingue.