1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikici a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Suleiman Babayo AH
December 9, 2025

Dubban mutane na ci gaba da tserewa daga yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, sakamakon rikicin da ke ci gaba da faruwa.

Gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Aubin Mukoni/AFP

Kimanin mutane 200,000 suka tsere daga gidajensu a yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango cikin kwanakin da suka gabata, sakamakon ci gaba da dannawa da 'yan tawayen kungiyar M23 da ke samun goyon bayan kasar Ruwanda suke yi, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta jagoranta.

Halin da ake ciki

Gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Hugh Kinsella Cunningham/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da sanarwar da ke nuna mutane 74 sun halaka yayin da wasu 83 suka jikata sakamakon tashe-tashen hankulan cikin kwanakin nan.

Wannan na zuwa bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya jagoranci saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ta kunshi shugabannin kasashen na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda gami da wasu shugabannin kasashen yankin.

Ita dai Ruwanda ta sha musanta cewa tana goyon bayan 'yan tawayen M23 na gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, amma Majalisar Dinkin Duniya tana da hujjojin da ke tabbatar da hannun Ruwanda cikin yakin da ke faruwa.