1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Duniya na jimamin mutuwar Jimmy Carter

December 30, 2024

Shugaba Joe Biden ya ayyana ranar tara ga watan Janairu na 2025 a matsayin ranar makoki a fadin Amurka domin girmama marigayi Jummy Cater wanda ya mutu yana da shekaru 100 a duniya.

Tsohon shugaban Amurka Jummy Cater ya mutu
Tsohon shugaban Amurka Jummy Cater ya mutuHoto: Dennis Van Tine/STAR MAX/IPx/picture alliance

Amurka na cikin alhinin mutuwar tsohon shugaban kasar Jimmy Carter wanda ya rasu a jiya Lahadi yana da shekaru 100 a duniya a mahaifarsa da ke Gojiya.

Jimmy Carter ya kasance shugaban Amurka na 39, kuma ya ja ragamar kasar daga shekarar 1977 zuwa 1981 bayan an zabe shi a 1976 inda ya yi wa'adi mulki guda daya.

A lokacin da yake raye ya yi futuka matuka gayya wajen shinfida zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya ciki har da jagorantar yarjejeniyar sulhu tsakanin Isra'ila da Masar a watan Maris na 1979.

Bayan saukarsa daga kan garagar mulkin fadar White House Jimmy Carter ya kafa gidauniyarsa ta Carter don ingantuwar zaman lafiya da magance rikice-rikice a duniya lamarin da ya kai shi ga lashe kyautar zaman lafiya ta Prix Nobel a shekarar 2002.

Tun bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban mafi shekaru a tsofin shugabannin Amurka, shugabannin kasashe da hukumomi na duniya na bayyana alhini tare da yaba masa bisa ayyukan alheri da ya yi a zamanin rayuwarsa.

Tuni ma Shugaba mai barin gado na Amurka Joe Biden ya ayyana ranar tara ga watan Janairu na 2025 a matsayin ranar makoki a fadin kasar domin girmama marigayi Jummy Cater.