Tsibirin Lampedusa
July 24, 2012Lampedusa tsibiri ne da ke ƙasar Italiya,tun shekara 1843 wato shekaru 170 kenan da suka gabata, wani yanki ne na cikin jihar Cicile.
Shekaru kimanin 20 bayan da Italiya ta mallaki Lampedusa ta baiwa wannan tsibiri matsayin ƙaramar hukuma.
A lokacin yaƙin duniya na biyu Italiya ta mayar da tsibirin wani sansanin sojojinta na ruwa ,saboda haka ne ma sojojin Amurika da abokan ƙawancensu su ka kai farmaki ga wannan tsibiri su ka yi kaca-kaca da rundunonin Italiya dake jibge a wurin, wanda shine ya basu damar cin jihar Cicile da yaƙi, zamanin yaƙin duniya na biyu.
A yanzu yawan mutanen dake zaune a Lampedusa sun kai kimanin dubu 600.Sannan wannan tsibiri ya na ƙarshen kudu na ƙasar Italiya kuma shine, kuma tare da tsibirin Cyprus Lampedusa na matsayin yankuna mallakar Turai na ƙarshen gabas.
Maƙwaftaka tsakanin Lampedusa da Afrika
Tsakanin Lampedusa da Tunisiya kilomita 167 ne kawai sannan kilomita 355 tsakanin wannan tsibiri da birnin Tripoli na ƙasar Libiya.
Kusanci da Tunisiya da kuma Libiya shine ya sa 'yan gudun hijira dake shigowa Turai ta ɓarauniyar hanya suke kwararowar a tsibirin Lampedusa, suna amfani da jiragen ruwa inda suke biyan kuɗaɗe masu yawa, domin a tsalla da su zuwa gaɓar arewa ta Teku.To saidai kamar ya sha bayana wa a cikin labarai da dama daga cikin 'yan gudun hijirar suna rasa rayuka a cikin wannan aikin kasada.
Hukumar ƙungiyar tarayya Turai mai kulla da yaƙi da shigowar baƙin haure ta bayana rahoto inda ta ce tun wajejen shekara 1992 aka fara samun shigowar baƙin haure ta tsibirin Lampedusa a ƙasashen Turai domin da zaran baƙin suka yi nasara shigowa Lampedusa za su iya shiga ko wace ƙasa ta Turai.Lampedusa na matsayin tundun muntsira.Kuma tun daga shekara ta 1992, har kullum yawan su nakara lunkawa, misali a shekara 2003 baƙin haure dubu takwas su ka shigo turai ta barauniyar hanya ta yi amfani da tsibirin Lampedusa a shekara 2004 yawan sai ya karu zuwa dubu 13 ya kai dubu 25 a shekara 2005,a shekara 2007 baƙin haure masu shigowa Turai ta ɓarauniyar hanya su kusan dubu 32 suka biyo ta Lampedusa.
Sannan tun lokacin da aka ƙaddamar da juyin juya hali a ƙasashen Larabawa musamman Tunisiya da Libiya Lampedusa ta yi maƙil da 'yan gudun hijira daga wannan ƙasashe biyu.Sun yi amfani da sassauci ta fannin binciken shigi da fici a ƙasashen Libiya da Tunisiya a lokacin ɓarkewar guguwar su ka yi ta kwarara zuwa Lampedusa, wannan matsala itace ma har ta sa wasu daga ƙasashen Turai suka bu kaci a gudanar da kwaskwarima ga yarjeniyar Schengen wadda ta bada damar walwalar zirga zirga tsakanin ƙasashen Turai da suka rattabama wannan yarjejeniya hannu.
Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu