1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Tsofaffin shugabannin Amurka za su halarci jana'izar Carter

January 9, 2025

An shirya gudanar da jana'izar ban girma ta marigayi tsohon shugaban Amurka na 39 Jimmy Carter a babbar majami'ar Washington DC, inda za a gabatar da addu'o'i da kuma jawabai masu ratsa zuciya.

Tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter
Tsohon shugaban Amurka Jimmy CarterHoto: Abaca Olivier Douliery/dpa/picture alliance

Shugaba Joe Biden zai gabatar da jawabi a harabar cocin Episcopal da ke kasancewa wajen da ake gabatar da jawabai kan kyawawan halayyar tsofaffin shugabanni wanda ke zama al'ada tun daga lokacin Dwight Eisenhower da Ronald Reagan har zuwa zamanin  George H.W. Bush.

Karin bayani: Tshohon shugaban Amurka Jimmy Carter ya mutu yana da shekaru 100

Tsofaffin shugabannin kasar Bill Clinton da George W. Bush da Barack Obama har ma da shugaba mai jiran rantsuwa Donald Trump za su halarci jana'izar tare wasu mutanen sama da 3,000. Za dai a binne Carter a kusa da kabarin matarsa Rosalynn Carter a mahaifarsa da ke Georgia.