1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsofaffin 'yan takarar Republican sun yi wa Trump mubayi'a

July 17, 2024

Dan takarar neman shugaban kasar Amirka na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya sake komawa babban taron jam'iyyar na kasa.

Tsofaffin 'yan takarar Republican sun yi wa Trump mubayi'a
Tsofaffin 'yan takarar Republican sun yi wa Trump mubayi'aHoto: Angela Weiss/AFP via Getty Images

Dan takarar neman shugaban kasar Amirka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya sake komawa babban taron jam'iyyar na kasa yayin da tsofaffin abokan takarar jami'yyar suka nuna goyon bayansu ga tsohon shugaban kasar.

Uku daga cikin tsofaffin 'yan takarar sun yi ta koda Shugaba Trump tare da nuna goyon bayansu karara, ciki kuwa har da tsohuwar jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta da yi ikrarin cewa hadin kan jam'iyyar zai ceto kasar. Shugaba Trump dauke da bandeji a kunnensa bayan raunin da ya ji a yunkurin kashe shi da aka yi, ya yi ta daga hannu ga jama'a tare da mika godiyarsa.