1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tsohon firaministan Nijar Hama Amadou ya rasu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim SB
October 24, 2024

Hama Amadou kwararren 'dan siyasa ne da ya yi aikin gwamnati tun lokacin mulkin shugaban kasa marigayi Seyni Kountche,sannan ya yi da tsofin shugabanni irin su Tanja Mamadou a 1995 da kuma Mahamadou Issoufou

Marigayi Hama Amadou
Marigayi Hama Amadou tsohon firaministan Jamhuriyar NijarHoto: Issouf Sanogo/AFP

Tsohon firaministan Jamhuriyar Nijar Hama Amadou ya rasu a daren Laraba, bayan fama da rashin lafiya, kamar yadda wasu makusantansa suka tabbatar. Wakilinmu na Yamai Salissou Boukari ya ce Hama Amadou wanda ya taba rike mukamin shugabancin majalisar dokokin kasar, ya rasu ne a kan hanyar kai shi babban asibitin birnin Yamai.

Karin Bayani:Madugun adawa Hama Amadou ya koma gida

Marigayi Hama Amadou tsohon firaministan Jamhuriyar NijarHoto: Boureima Hama/AFP

An haifi marigayi Hama Amadu ranar 3 ga watan Maris din shekarar 1950, a garin Youri da ke cikin jihar Tillabery, a yammacin Jamhuriyar Nijar, inda ya bar duniya yana da shekaru 74.

Karin bayani:Tsohon Shugaba Issoufou ya juya wa Bazoum baya

Hama Amadou kwararren 'dan siyasa ne da ya yi aikin gwamnati tun lokacin marigayi shugaban kasa Seyni Kountche, inda ya rike mukamin firaminista a lokacin mulkin marigayi Tanja Mamadou a 1995, kafin ya zama shugaban majalisar dokoki a lokacin mulkin shugaba Mahamadou Issoufou, daga bisani kuma aka tilasta masa yin gudun hijira, wanda sai bayan juyin mulkin sojoji ne ya samu sukunin koma wa kasar ba tare da wata matsala ba.