1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaduna: Rasuwar Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa

November 11, 2020

Al'umma daga sassan Najeriya sun halarci jana'izar tsohon gwamnan Kaduna na farko farar hula a yayin mulkin Jamhuriya ta biyu Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa da Allah ya yiwa cikawa.

Nigeria

Daga cikin wadanda suka halalci jana’izar har da tsoffin gwamnonin Jihar Kaduna da wakilan gwamnatin jihar da tsoffin ‘yan takarar shugabancin kasa hadi da malaman addinai da sarakunan gargajiya. Alhaji Balarane Musa mai shekaru 84 a duniya ya rasu bayan wata gajeruwar rashin lafiya a Kaduna kuma bar yara tara da mata daya. Balarabe Musa ya yi gwamnan Kaduna a tsawon shekara guda, cikin tsukin lokacin da yana gwamna ya gina manyan kamfanoni da masana'antu kamar su kamfani nika Tomatur dake Ikara a gabanin tsigeshi daga mukamin. Kamin rasuwar sa ya kasance Jagoran jam'iyyar People Redemption Party (PRP-Nasara). Kuma Sagiru Balarabe Musa daya daga cikin ‘ya’yan marigayin ya bayyana rasuwar mahaifin su a matsayin babban rashi a Najeriya duba da yadda har ya rasu yake fafutikar tabbatar da dimukuradiyya da yaki da cin hanci da rashuwa a Najeriya. 

Daga cikin wadanda suka halalci janai’azar har da tsohon gwamnan Kaduna Alhaji Muktar Ramalan Yaro wanda ya ce akwai kyawawan abubuwa da daukacin ‘yan siyasar arewacin Najeriya za su koya na daga halayyar marigayin. "Ba zan manta da gudunmawar da ya bayar wajan ci-gaban kasa da tabbatar da dorewar mulkin Dimukuradiyya." Daya daga cikin 'yan siyasar Kaduna Alhaji Isa Ashiru ya bayyana marigayin a matsayin mai kishin talakawa, a yayin da Honorable Bashir Saidu kwashinan kudi na jahar Kaduna ya nuna cewa jihar ta yi hasarar dattijo. Shugaban Muhammadu Buhari, ya mika sakon ta'azziya ga daukacin al'ummar Jihar Kaduna bisa rashin tsohon gwamnan.