1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon madugun yakin Laberiya ya rasu

November 28, 2024

Mutumin da ya jagoranci yakin kasar Laberiya na tsawon shekaru 14, bar duniya a wannan Alhamis. Prince Johnson wanda ya yi kaurin suna a yakin da ya durkusar da kasarsa ya sake shiga harkokin gwamnati kafin mutuwarsa.

Marigayi tsohon madugun yakin Laberiya, Prince Johnson
Marigayi tsohon madugun yakin Laberiya, Prince JohnsonHoto: picture-alliance/G.Osodi

An ba da labarin mutuwar tsohon madugun yakin Laberiya, Prince Johnson, mutumin da ya aikata mumunar ta'asa lokacin yakin basasar kasar a tsakanin shekarun 1989 zuwa 2003.

Prince Johnson, wanda daga bisani ya taka rawa a siyasar Laberiya, inda ya zama dan majalisar dattawa; ya mutu ne a ranar Alhamis yana da shekaru 72.

A cikin shekara 1990 wani faifan bidiyo ya nuno Johnson na kurbar barasa lokacin da mayakansa ke azaftar da marigayi Shugaba Samuel Doe har ya sheka lahira.

Kisan na tsohon shugaban Laberiya Samuel Doe ne dai ya zamo silar fadawar kasar cikin yakin basasar da ta yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane dubu 250, sannan kuma ya yi matukar ruguza tattalin arzikin kasar.