1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Jigon NPP ya fice domin takarar shugaban kasa

September 26, 2023

Tuni dai wannan mataki ya haifar da shakku a jam'iyyarsa ta NPP wacce ya yi watsi da ita, inda masana siyasa ke hasashen matakin ka iya karya lagon jam'iyyar a zaben watan Disamba na shekara mai zuwa.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Hoto: Nipah Dennis/AFP

Tsohon ministan kula da harkokin kasuwanci da masana'antu na kasar Ghana Alan Kyeremanten ya ce ya shirya ficewa daga jam'iyya mai mulkin kasar domin tsayawa takarar shugaban kasa a matsayin dan takara mai cin gashin kansa.

Tsohon ministan wanda jigo ne a jam'iyyar NPP ya yi zargin jam'iyyar ba ta nuna godiya ga irin gudunmawar da yake ba ta. A cewar sa, dalilin da ya tilasta masa murabus daga mukamin minista a farkon shekarar nan ke nan. Dan siyasar dai ya ce sabuwar tafiyar tasa cike take da matasan kasar Ghana da ke da muradin ganin an samar da sauyi a kasar. Jam'iyyar ta NPP ta kira matakin tsohon ministan a matsayin abin takaici.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani