1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ya tsallake rijiya da baya

March 30, 2024

Wani hadarin mota ya rutsa da tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, inda bangaren hamayya ta zargi gwamnati mai ci da kitsa hadarin da ya kasance na biyu da ke kama da juna.

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma
Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob ZumaHoto: EMMANUEL CROSET/AFP

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya, a wani hadarin mota da wani da ya yi mankas da barasa ya haddasa.

To sai dai kuma jam'iyyar da ya assasa ta yi zargin jam'iyyar ANC mai mulki karkashin ikon shugaban kasar na yanzu Cyril Ramaphosa da kitsa hadarin ta hanyar yin amfani da mashayi da ya yi tatil.

Cikin kalamansa, kakakin tsohon shugaban na Afirka ta Kudu, ya ce ba zai yiwu a samu hadura masu kama da juna har sau biyu da ke kutsawa cikin ayarin motoci Mr. Jacob Zuma ba.

Hadarin ya faru ne dai sa'o'i bayan jami'an zabe sun dakatar da Mr. Zuma daga tsayawa zaben watan Mayu, abin kuma da haddasa hargitsi.

A shekara ta 2028 ne dai aka tilasta wa tsohon Shugaba Zuma, wanda dadadde ne a jam'iyyar ANC ficewa daga cikinta saboda zargin aikata almundaha da dukiyar kasa.