1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Tsohon shugaban Amurka Trump zai sulhunta Ukraine da Rasha

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 27, 2024

Mr Trump ya bayyana cewa da shi ne ke kan kujerar shugabancin Amurka, Rasha ba za ta mamayi Ukraine ba

Hoto: Evan Vucci/dpa/AP/picture alliance

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump zai gana da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a safiyar wannan rana ta Juma'a, domin tattauna halin da kasar ke ciki kan yakinta da Rasha, inda Trump din ke ikirarin cewa yana da hanyoyin sulhunta kasashen biyu.

Karin bayani:Ministocin NATO na taro kan shirin tallafa wa Ukraine

Jagogrin biyu za su gana ne a ofishin tsohon shugaban na Amurka wato Trump Tower da ke birnin New York, ganawar kuma na zuwa ne kwana guda bayan da Mr Zelensky ya yi tozali da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris, wadda ke takarar shugabancin Amurka da Trump, har ma ta ba shi tabbacin cikakken goyon bayanta gare shi.

Karin bayani:Makomar tallafin soja a Ukraine

Mr Trump ya bayyana cewa da shi ne ke kan kujerar shugabancin Amurka, to babu ta yadda za a yi Rasha ta kai harin mamaya ga Ukraine, kamar yadda ya sanar ranar Alhamis. 

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ne da kansa ya nemi ganawa da 'dan takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Repulican din, kamar yadda Mr Trump ya sanar.