Tsohon shugaban Burkina Faso ya nufi Marokko daga Cote d'Ivoire
November 20, 2014Talla
Wani kakakin gwamnatin Cote d'Ivoire ya ce tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore wanda aka tilasta masa sauka daga kan karagar mulki biyo bayan wani bore, ya bar mafakarsa ta wucin gadi da ke Cote d'Ivoire, kuma ya doshi kasar Marokko inda zai yi kaura. Bruno Kone kakakin gwamnatin Cote d'Ivoire ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa Compaore wanda ya kwashe shekaru da yawa a kan kujerar shugabancin Burkina Faso, ya yanke shawarar sauya mafakarsa zuwa Marokko. Kakakin ya kara da cewa a kullum kofofin kasarsa a bude suke ga Blaise Compaore.