1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Tsohon shugaban kasar Aljeriya ya rasu

September 18, 2021

An sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar Aljeriya, Abdoulaziz Bouteflika, wanda ya kwanta dama, bayan kwashe shekaru da ya yi yana fama da rashin lafiya.

Algeria Germany
Hoto: Sidali Djarboub/AP/picture-alliance

Marigayi tsohon shugaban Aljeriya, Abdoulaziz Bouteflika, wanda shi ne ya fi dadewa a kan karagar mulki a Aljeriya, ya mutu ne a ranar Juma'a kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Ya jagoranci kasar na wa'adi hudu daban-daban, da ya kai shekaru 20 na tsawon mulkinsa.

Albdoulaziz Bouteflika ya fuskanci bore daga 'yan kasar wanda ya tilasta masa sauka daga mulki a 2019, saboda kokarin da ya yi na neman zarcewa karo na biyar.

A shekara ta 2011 ma dai marigayin marigayin shugaban na Aljeriya wanda dan darikar Qadiriyya ne, ya fuskanci wani gagarumin bore, sai dai ya sha a lokacin.

Shugabannin kasashen yamma sun yaba kokarinsa wajen yaki da 'yan bindiga inda ke nuna yarda da manufofinsa na yaki da ta'addanci.

Abdozulaziz Bouteflika ya yi fama da shanyewar barin jiki tun cikin shekara ta 2013, cutar da ta hana shi iya fitowa bainar jama'a na tsawon lokaci.